
Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya gargadi masu zanga-zanga da su nesanci birnin tarayya.
Wike ya bayyana wa manema labarai haka ne bayan ganawa da jami'an tsaro a Abuja a jiya Alhamis.
Ministan ya ce, duk da cewa 'yan Najeriya sunada 'yancin gudanar da zanga-zanga lumana, amma ba a birnin tarayya ba.
Ministan dai ya buya da ayyana ranar 1 ga watan Agusta ta zama ranar gudanar da bikin karrama sarakunan gargajiyan yankin birnin na tarayya don kassara zanga-zangar.
Yayin da ya kai ziyarar bude wani aikin a yankin Saburi a Kubuwa dake birnin tarayyar, Wike ya ja hankalin mutane da su kauracewa zanga-zangar 'yan fashi da makami.
Ya ce, zanga-zangar da aka shirya aikin hannun bata gari ne, ba masu kishi ko son kasar ba, don haka, jama'a suyi hankali.