
Mai martaba sarkin Rano a jihar Kano arewa maso yammacin Najeriya Muhammadu Isa Umaru ya roki gwamna Abba Kabir Yusuf ya soke kwangilar gina titi a yakin na Rano.
Sarkin ya roki gwamna da ya mika kwangilar ga wani mutum domin samun nasarar kammala aikin cikin lokacin da ya dace.
Sarkin ya ce dan kwangilar da aikin ke hannunsa bazai iya gama aikin na Naira miliyan 5 akan lokaci ba, don haka, akwai bukatar a karbi kwangilar daga hannunsa.
Sarkin ya furta haka ne yayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ke nada mishi rawani da bashi sandar sarautar Rano.
Sarkin mai daraja ta biyu ya kuma roki gwamnan da ya kawo karshen matsalar rashin ruwan sha da ke addabar yankin na Rano wanda gwamnatocin da suka gabata suka gaza warware ta.