• 17 Jun, 2025

Sarkin Kano Khalifa Sanusi Ya Gargadi Alkalan Manyan Kotun Najeriya Kan Muhimmancin Adalci

Sarkin Kano Khalifa Sanusi Ya Gargadi Alkalan Manyan Kotun Najeriya Kan Muhimmancin Adalci

1000009595.jpg

Mai martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya shawarci alkalan kotun kolin Najeriya da su yi Shari'a bisa adalci sa tsoron Allah.

Muhammad Sanusi na biyu ya ce, Akwai ranar da alkalan za su tsaya a gaban Ubangiji su yi bayani kan yadda su ka gudanar da harkokin Shari'a yayinda su ke duniya.

Sarkin Kano ya furta hakan ne yayinda ya ke jawabi a wajen wani taro a birnin Legas mai taken "doka da ka'idojin aikin Shari'a da kyawawan dabi'u."

An gudanar da taron ne domin girmama mai Shari'a Habeed Abiru wanda ya samu karin girma zuwa alkalin kotun kolin Najeriya.

Sarki Sanusi ya ce, akwai bukatar alkalan su yi taka-tsan-tsan kan yadda su ke gudanarda harkokin Shari'a a kasar, inda ya ce ya kamata su zama masu adalci a kowani lokaci.

Sanusi Lamido Sanusi ya gargadi alkalan da su guji bawa masu laifi gaskiya domin Ubangiji na hushi da hakan.

A nata jawabin, babbar mai Shari'a ta kasa Kudirat Kekere-Efun, ta ce, alkalan kotun kasar na iya kokarinsu wajen yin abinda ya kamata ta fuskar adalci a Shari'u, amma akwai kadan daga cikin su da ke bata aikin alkalancin a Najeriya.

Mai Shari'ar Kudirat ta shawarci alkalan da su yi adalci domin kare kansu a gaban Ubangiji ranar kiyama.

Kudirat ta ce, akwai bukatar cikakken 'yancin alkalan kotun kasar domin  gudanarda ayyukan su yadda ya kamata, batare da tsangwama ba.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.