
Sama da yara 100 ne ba sa zuwa makaranta sakamakon lalacewar makarantar Firamare da ke Ledi 2 a Gwagwalada cikin birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Azuzuwa da rufin azuzuwan sun lalace tsawon wani lokaci, yayinda babu kujerun zama domin koyon darusa, lamarin da ya tilasta yaran zama a gidajen iyayensu.
Wata kafa mai sa ido kan ci gaban kasa ce ta bankado matsalar, inda ta shawarci ministan Abuja Nyesom Wike da 'yar majalisar dattawa mai wakiltan Abuja Ireti Kingibe da su kawo karshen matsalar.
Shugaban kafar Illevbaoja Uadamen ya ce, abin takaici ne yadda gwamnatin kasar ta lalace ta hanyar gaza daukan nauyin da ke kanata.
Uadamen ya kara da cewa maimakon gwamnati ta maida hankali wajen samarda ilimi, sai kashe kudade kan abubawa marasa kan kado.
Uadamen ya ce, abubuwan ci gaba talakawa ke bukata musamman ilimin yara daga gwamnati, amma hakan ya gagara daga mahukuntan kasar.
Makarantu musamman na Firamare a Najeriya na fuskantar matsalolin rashin kulawa musamman azuzuwansu da biyan malamai albashi.
Lamarin na faruwa a jihohin kasar da dama, wanda hakan babbar barazana ce ga harkar ilimi, yayinda hakan tauye hakkin ilimin yara ne.
Abin jira a gani dai shi ne yiwuwar daukan matakan gaggawa domin ceto goben yaran da ba sa zuwa makaranta, ta hanyar gyara makarantan Firamaren da ke babban birnin kasar Abuja.