
An gudanar da jana'izar mutanen da suka halaka sakamakon fashewar wata tankar mai a jihar Jigawa.
Kawo yanzu dai hukumomi sun ce wadanda suka mutu sun kai 104, inda sama da 100 kuma suka jikkata.
Shaidu sun ce tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.
Mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar mai a jihar Jigawa sun karu zuwa 104.
Shugabar hukumar kiyaye hadura ta jihar Jigawa, Aishatu Sa'adu ce ta tabbatar da hakan.
Ta ce kawo yanzu fiye da mitum 100 kuma suna asibiti saboda raunuka da suka samu, inda suke karbar magani.