
Sabon ministan ilimin Najeriya Dakta Olatunji Alausa ya yi fatali da tsarin da tsohon minista Tahir Mamman na ka'idar shekarun shiga jami'a.
Tsarin da tsohon ministan ilimin Mamman ya kawo ya janyo cece-kuce a fadin Najeriya, inda ministan ya ce sai mutum na da shekaru 18 kafin za a bashi damar shiga jami'a.
Ministan Alausa ya sanarda watsi da tsarin Tahir Mamman ne jiya Talata yayinda ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.
Alausa ya ce tsarin tsohon ministan koma baya ne a harkar ilimi a Najeriya, inda yace hakan zai hana yan kasar damar karatu a lokacinda ya kamata.
Minista Olatunji Alausa ya bayyana cewa yan Najeriya masu shekaru 16 daga yau za su samu damar shiga jami'a a kasar.
Alausa ya kara da cewa akwai tanadi na musamman ga masu baiwa wadanda suka samu sakamakon jarabawa mai kyau.
Ministan ya kara da cewa nan ba da dadewa ba za su kawo tsarinda zai bada damar fara amfani da abinda mutum yake da shi a kwakwalwa ba a rubuce ba.
Sabon ministan ilimin Alausa na daga cikin sabbin ministoci 10 da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada bayan ya yi sauye-sauye a majalisar ministocin a watan Oktoba.