
Majalisar wakilan Najeriya ta rantaba hannu kan kudurin dokar sabon albashi mafi kankanci na Naira dubu 70.
Fadar shugaban kasar Najeriya ta amince da albashin inda ta aikawa majalisar don sa hannu.
Ana sa rai dai biyan sabon albashin na N70,000 zai fara aiki ne daga watan hudu.
A lokaci guda, majalisar ta wakilai ta sa hannu kan bukatar fadar shugaban kasa na karin kasafin kudi don fadada Ayyukan gina kasa.
Fadar shugaban kasar dai ta bukaci karin kudi Naira Triliyan 6.2 a kan kasafin kudin bana a makon da ya gabata. A yanzu haka jimillan kasafin kudin shekarar 2024 ya kai Naira Triliyan 35.5.