• 18 Jun, 2025

Rundunar 'Yansandan Kano Sun Kama Yara Kanana 40 Wadanda Shari'a Bata Hau Kansu Ba Lokacin Zanga-Zanga

Rundunar 'Yansandan Kano Sun Kama Yara Kanana 40 Wadanda Shari'a Bata Hau Kansu Ba Lokacin Zanga-Zanga

fb-img-17244962319476053-1.jpg

Rundunar 'yansandan jihar Kano ta ce ta cafke mutum 873 sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da yan kasar suka gudanar a sassan kasar farkon wananan watan.

Rundunar ta ce ta gurfanar da wadanda ake zargi da yin zanga-zangar gaban kuliya a kotun magistrates daban-daban a fadin jihar. 

Rundunar ta ce ta sallami yara da ta kama yayin zanga-zangar domin doka ba ta bada damar a yi musu sharia ko tusa keyar su gidan kaso ba.

Amma rahotanni sun nuna cewa rundunar 'yansandan sun saki kananan yaran ne bayan matsin lamba da suka fuskanta daga wata kungiyar kare hakkin bil'adama wanda lawya AK Musa ya jagoranta.

AK Musa ya shaidawa manema labarai cewa yara 40 ne suka kubuto daga hannun 'yansansan bayan da farko an tura su gidan yari.

Lawyan ya kara da cewa sauran mutanen da aka kama suna gidan maza inda aka hana bada belin su.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.