
Rundunar 'Yansandan Jihar Borno ta ce, ta yi nasarar kassara wasu kayan fashewa da ta gano a unguwannin Dala da Gwange da ke birnin Maiduguri.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin tabbatarda tsaron jama'a da dukiyarsu, inda ta ja hankalin al-umma da su zama masu kulawa yadda ya kamata.
Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan'sandan jihar, ASP Grace Michael ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta sawa hannu a jiya Asabar, inda ta ce, sun samu nasarar dakile ababen fashewan ne bayan mutanen unguwannin biyu sun kirasu akan lokaci ranar Juma'a da safe.
Grace ta kara da cewa, sun samu rahoton ganin ababen fashewan ne misalin karfe takwas na safiyar Juma'a a unguwan Dala, Abujan Talakawa, a kusa da wani gida da ba a kammala shi ba.
Michael ta ce, nan take suka tura mutum 13 daga rukunin warware bama-bamai na rundunar, inda aka samu ababen fashewa shida da bam guda daya, yayinda aka samu rahoto na biyu misalin karfe 1 na rana a Gwange, duka a birnin Maiduguri.
Grace ta yaba hubbasan mazauna unguwannin biyu, inda ta ce, wajibi ne a kansu su kare lafiyar jama'a a duk inda su ke, inda ta kara da cewa, mutane su ci gaba da kulawa da bawa rundunar 'yansandan bayanai idan su ka ga wata alama ta rashin tsaro.