• 18 Jun, 2025

Rundunar Sojojin Najeriya Sun Hallaka 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Rundunar Sojojin Najeriya Sun Hallaka 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara

fb-img-17262285863670775.jpg

Rundunar hadin gwiwa ta sojojin Najeriya mai lakabi da Hadarin Daji sun kassara 'yan bindiga da Kachalla Buzu ke jagoranta a yankin kauyen Mayanchi da ke jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojan sun hallaka 'yan bindigan da dama tare da kwace makamai da babura a jiya Alhamis.

Sojojin Najeriya sun shirya wa 'yan bindigan kwanton bauna inda suka yi nasarar kashe su tare da shugaban su  Kachalla Buzu.

An ci nasarar kashe 'yan ta'addan ne sakamakon bayanan sirri da sojojin suka samu akan 'yan bindigan.

A kalla babura 30 da makamai masu yawa sojojin suka kwato daga hannun 'yan bindigan bayan sun yi nasarar hallaka su.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun rufe titin Gusau zuwa Funtuwa inda suka yi garkuwa da mutane da dama kafin rundunar sojojin su kassara su.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.