• 18 Jun, 2025

Rundunar Sojin Najeriya Ta Gargadi Masu Shirin Zanga-Zanga

Rundunar Sojin Najeriya Ta Gargadi Masu Shirin Zanga-Zanga

Rundunar Sojin Najeriya Ta Gargadi Masu Shirin Zanga-Zanga

screenshot-20240725-171134-1721923919782.jpg

Cibiyar tsaro ta sojin Najeriya wato
Defence Headquarters, ta gargadi masu shirin fara Zanga-zanga da su guji wuce gona da iri.

Cibiyar tsaron ta ce, tana sane da 'yancin 'yan Najeriya kan Zanga-zanga, amma ba za ta zuba idanu ta bari mutane su lalata kasa ba.

Yayin ganawa da manema labarai a Abuja, mai magana da yawun cibiyar rundunar Manjo-janar Edward Buba ya ce, sojin Najeriya za su sa ido yadda ya kamata yayin gudanar da zanga-zangar domin kaucewa karya doka da oda.

Sojojin sun ja kunnen masu zanga-zangar da suyi taka-tsan-tsan a yunkurin su na nuna rashin dadin su da gwamnatin kasa.

A ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa ne 'yan Najeriya suka shirya fitowa yin Zanga-zangar nuna rashin gamsuwar su da gwamnatin Najeriya.

'Yan Najeriya sun ambaci wahalhalu da suke ciki na talauci da yunwa biyo bayan cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi, da ma mummunar cin hanci da rashawa tsakanin jami'an gwamnatin kasar da dai sauransu.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.