
Rundunar sojan Najeriya ka iya rasa manyan hafsoshin ta da dama sakamakon wani kudurin tsari doka da zai kara musu yawan skekaru kafin samun karin girma.
Idan shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu a sabon kudurin, manyan sojojin kasar da suka shiga aikin soja ta gajeruwar hanya wato short service a turance, za su samu karin shekaru kafin samun karin anini.
Sakamakon wannan yunkurin, manyan sojojin kasar sun yi gargadin cewa rundunar za ta rasa sojoji da dama, domin da yawan su za su bar aiki, wanda hakan babbar asara ce garesu da ma kasa baki daya.
Amma sabon tsarin dokar ba za ta shafi wadanda suka shiga aikin sojan tun daga farko ba musamman wadanda suka shiga ta makarantar soja ta NDA.