• 18 Jun, 2025

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kama Mai Hannu A Kisan Shugaban Miyetti Allah

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kama Mai Hannu A Kisan Shugaban Miyetti Allah

cds-major-general-christopher-musa-e1688087345500-1.jpg

Rundunar sojan Najeriya ta cafke dan ta'adda da ke da hannu cikin kisan shugaban Miyetti Allah na jihar Oyo Mairuga Abubakar.

Sojojin Najeriyan sun kuma kama wani mai safara wa yan bindiga makamai da albarusai wanda na daga cikin masu hana arewa maso yammacin kasar zaman lafiya.

Rundunar sojin har wayau ta kama wani dan bindigan da makamai da jigidan albarusai a wani samame na daban duka a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Sojin kasar ta ce ta samu nasarar kama yan ta'addan ne a wani aiki na musamman da takeyi domin dakile bata garin.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da hubbasa tare da hadin gwiwan sauran jami'an tsaro don ganin ta kawo karshen rashin tsaro a yankin baki daya.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.