
Rundunar sojan Najeriya ta bijirewa umarnin kotu, inda haryanzu ta ke tsare da dilolin shanu 15 a Abuja har tsawon watanni, sannan ta taba wasu daga cikin shanu 341da kudi Naira miliyan 88, 737, 200 da ta kwace a hannun 'yan kasuwan duk da umarnin da kotu ta bada.
Lauyan dilolin shanun Barista Abdulwahab Aliyu ya ce, rundunar sojan ta kama masu saye da sayarwan shanun ne 12 tun ranar 17 ga watan Mayu yayinda su ke kan hanyarsu ta zuwa sayan shanu a kauyukan jihar Borno.
Lauyan ya ce, babu laifin da 'yan kasuwan su ka yi, kawai an gansu da miliyoyin kudade ne da rana aka kama su tsakanin kauyukan Buratai da Mirngha, da ke karamar hukumar Biu, a jihar ta Borno.
Abdulwahab wanda shine lauyan da ya tsayawa wadanda ake zaluntan ya kara da cewa, babu makami ko wani abu na laifi da aka kama 'yan kasuwan da su, bayan kudi da aka samu a hannunsu na kasuwanci.
Rundunar sojan da ke rukunin JTF a cewar Abdulwahab sun nemi cin hanci ne daga dilolin shanun amma ba su samu ba, shi ne babban dalilin da ya sa suka kama su, suka karbe kudin, a karshe su ka tsare su na tsawon watanni.
Abdulwahab Aliyu ya ce, da farko sun ajiye su a kauyen Buratai, daga baya su ka dauke su zuwa Damaturu, sannan zuwa Maiduguri. Abdulwahab ya ce, daga bisani sun tsare su a magarkamar soja da ke barikin Giwa a Maiduguri.
Baristan ya ce, an ci zarafin wasu daga cikin su ta hanyar azabtar da su ba tare da laifi ba yayinda sojojin ke yi musu tambayoyi domin su amsa laifin ta'addancin da sojojin ke son lakaba musu domin 'yan kasuwan su bar musu shanu da kudaden da suka karbe.
Aliyu ya ce, daga karshe 'yan kasuwan sun je babbar kotun jihar Borno domin neman 'yancin su, inda su ka yi nasarar samun adalci aranar 6 ga watan Agusta.
Barista Abdulwahab ya ce sun yi nasara sakamakon hukuncin kotu, inda ta ce rundunar sojan ta tsare su ne ba bisa ka'ida ba, inda kotun ta bukaci sojojin su kai su gabin kuliya cikin kwanaki 7 idan sunada wata hujja na laifi akan mutanen da su ka kama.
Babban kotun ta bada umarnin bada belin 'yan kasuwan kuma ta bada umarnin basu kudadensu da shanunsu da tarar tsare su ba bisa ka'ida ba na Naira Miliyan 10 ga kowani daya daga cikinsu.
Abin mamaki a cewar Barista, rundunar sojan ta JTF sun yi watsi da umarnin kotun, inda haryanzu ba su saki mutanen ba kuma ba su basu dukiyoyinsu kamar yadda kotu ta umarce su ba.