
Shugaban hafsan sojan kasa na Najeriya ya bada umarnin gudanarda bincike kan wani bidiyo da ke nuna yadda sojoji su ka cin zarafin wani mutum da matarsa.
Bidiyon da ya karada yanar gizo ya nuna yadda wasu sojoji masu tsaron wani Manjo Janar ke dukan wani mutum da matarsa a cikin mota.
Sojojin sun ci zarafin ma'auratan ne bisa laifin wuce tawagar motocin Janar din sojan, wanda babu doka a Najeriya da haramta yin hakan.
Hoton bidiyon ya nuna yadda wani babban soja da wani karami ke dukan mutumin a cikin mota, inda suka daki matarsa sakamakon kokarin daukar horon abinda ke faruwa.
Rahotanni sun tabbatarda da cewa tawagar ta Manjo Janar G. S. Mohammed ne da masu tsaronsa kofur A. Abubakar da wani sojan cikin kaki wadanda hoton bidiyon ya nuna fuskokinsu.
Binciken ya nuna yadda sojojin su ka ci zarafin mutumin mai suna Vershima Mker da mai dakinsa Lami Jennifer Iorvihi dukkansu a cikin motar a birnin tarayya Abuja.
Hoton bidiyon sun nuna yadda sojojin suka fitarda ma'auratan daga cikin motarsu, sa'annan suka yi musu wulakanci, bayan mijin ya wuce tawagar motocin da ke dauke da Manjo Janar Mohammed.
Bayan anci zarafin ma'auratan, sai kuma aka sa musu ankwa a hannayensu, inda sojojin suka jefa su a cikin wata motarsu kamar buhunan hatsi, su ka kaisu ofishin 'yansandan Gwarinpa da ke Abuja.
Manjo Janar na sojan ya bawa 'yansandan umarnin kulle mutanen biyu mata da mini ba tare da bada belinsu ba, har sai ya bada umarnin sake su.
Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce, rundunar na sane da abinda ya faru, bayan sun yi bitar bidiyon.
Nwachukwu ya kara da cewa, tuni shugaban hafsan sojan kasan ya bada umarnin bonciken lamarin domin daukan mataki.