• 17 Jun, 2025

Rundunar Sojan Najeriya Sun Kalubalanci Tsohon Shugaban Tsirarun Naija Delta Kan Barazanar Da Ya Yi Na Kakkabo Jirgin Saman Soja

Rundunar Sojan Najeriya Sun Kalubalanci Tsohon Shugaban Tsirarun Naija Delta Kan Barazanar Da Ya Yi Na Kakkabo Jirgin Saman Soja

1000001272.jpg

Hedikwatar tsaron Najeriya ta kalubalanci tsohon shugaban tsirarun Naija Delta Alhaji Asari Dokubo da ya tunkari rundunar sojojin kasar ya ga abin mamaki.

Rundunar sojan kasar ta ce za ta nuna mishi karfin ta idan ya na gani akwai ribar yin hakan.

Martanin rundunar tsaron ya biyo bayan barazanar da Mujahid Dokubo Asarin ya yi wa sojojin Najeriya ranar 5 ga wannan watan, inda ya ce zai kakkabo jirgin sojan Nigeria mai saukar ungulu.

Asari Dokubo ya yi alwashin yin hakan ne a cewar sa idan jirgin sojan mai saukar ungulu ya ci gaba da zirga-zirga a saman gidan sa.

Sakamakon barazanar da ya yi ne mai magana da yawun hedikwatar tsaron kasar Manjo Janar Edward Buba ya maida martani, inda ya ce suna daidai da zamanin Asari Dokubo.

Edward Buba ya kara da cewa akwai bambanci tsakanin soja da shi karamin kwaro. Buba ya ce idan Asari Dokubo ya raina rundunar sojan Najeriya ya fito ya gwada.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.