
Daya daga cikin manyan kamfanonin sufurin jiragen saman Najeriya Azman Air ya sanar da dakatar da ayyukan sa na jigilar matafiya sai yadda hali yayi.
Kamfanin Azman na daga cikin kamfanonin jiragen sama da sukayi fice a Najeriya musamman a tafiye-tafiyen cikin gida.
Kamfanin ya dauki irin wannan matakin a watan Agustan shekara ta 2023 inda ya ce rashin isassun jirage ne makasudin yin haka, yayin da ya bawa ma'aikatan sa hutu batare da biyan su albashi ba.
A wannan shekarar ma tarihi ya maimaita kansa inda katafaren kamfanin ya dakatar da ayyukan sa amma wannan karon sakamakon rashin darajar Naira.
Kamfanin ya bayyana cewa mafi yawancin abubuwan da yake amfani da su da Dala ya ke saya. Ya ce a yanzu haka yanayin babu kyau da kamfanin zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa.