• 18 Jun, 2025

Rana Ta Uku Ta Zanga-zanga A Birnin Lagas

Rana Ta Uku Ta Zanga-zanga A Birnin Lagas

screenshot-20240803-102423-1722678459555.jpg

Daruruwan mutane sun fito tituna a birnin Legas a rana ta uku ta zanga-zangar matsin rayuwa da talakan kasar ke ciki a yankin Ojota dake birnin.

Masu zanga-zangar karkashin kungiyar  #TakeItBackMovement sunce babu gudu babu ja da baya a kokarin su na neman saukin rayuwa a Najeriya.

Matasan dake dauke da kwalaye suna gudanar da zanga-zangar lumana don samun biyan bukatun su da gobe mai kyau daga gwamnatin Bola Tinubu.

A wani lamari da ya shafi zanga-zangar kuma, yan Najeriya su na ci gaba da nuna damuwar su kan yadda mahukunta suke hana masu zanga-zangar fita tituna a sassan kasar dake da jihohi 36.

Duk da haka, yan kasar sun ci gaba da anniyar su ta zagaya titunan biranen kasar domin gudanar da zanga-zangar cikin yanci da walwala.

 

 

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.