• 18 Jun, 2025

Raba Wa Masu Jin Yunwa Taliya Ba Shi Ne Mafita Ba — Cewar Tsohon Shugaban Kasa Abdussalami Abubakar

Raba Wa Masu Jin Yunwa Taliya Ba Shi Ne Mafita Ba — Cewar Tsohon Shugaban Kasa Abdussalami Abubakar

screenshot-20240918-082618-1726644406402.jpg


Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Abdussalam Abubakar ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda 'yan Najeriya ke fama da wahala a kasar.

Abubakar ya ce 'yan kasar na fama da wahalhalu matuka domin samun abin sa wa a baka sakamakon matsin tattalin arziki.

Tsohon shugaban ya kara da cewa lamarin wahalhalun da talakan kasar ke ciki ya fara wuce hankali.

Abdussalam Abubakar ya furta haka ne yayin da ya ke jawabi a cikin gidan sa da ke birnin Minna a jihar Naija a lokacin da ya marabci 'ya'yan wata kungiyar kare dimukradiyya da 'yancin bil'adama.

Janar Abubakar ya ce kowa a kasar na kukan wahalar yadda zai samu abincin da sauran kananan bukatun yau da kullum na dan adam, wanda hakan babban barazana ce a kasa kamar Najeriya.

Abdussalam ya ce abin takaici ne idan dan Najeriya ba zai iya cin abinci sau uku a rana ba sakamakon hauhawan kayayyakin masarufi da tsadar man petur da sauran su.

Janar Abdusdalam ya ce raba abinci da gwamnatin tarayya ke yi ba shi ne mafita ba. Ya zama dole gwamnati ta fitar da wani tsari da zai kawo saukin lamura.

Janar din sojan ya ce maimakon raba taliya, ya kamata gwamnati ne ta saya kayan abinci musamman hatsi da shinkafa ta sayar wa talaka akan farashi mai sauki yadda kowa zai iya saya ba raba abinda bai taka kara ya karya ba.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.