• 17 Jun, 2025

Peter Obi Ya Jinjinawa Aliko Dangote

Peter Obi Ya Jinjinawa Aliko Dangote

Peter Obi Ya Jinjinawa Aliko Dangote

peter-obi.png

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour a zaben shekara 2023 Peter Obi ya yaba kokarin hamshakin Attajirin dan kasuwan nan Aliko Dangote kan gina katafaren matatar mai a Najeriya.

Peter Obi ya ja hankalin Dangote da cewa kada ya kula da masu yi mishi gwalo kan gina matatar man domin abinda ya yi abu ne mai kyau da ka iya kawo canji a harkar mai a Najeriya.

Peter Obi wanda tsohon gwamnan jihar Anambara ne kudu maso gabashin kasar ya futa hakan ne ta shafin sa ta Twitter, inda ya karfafawa Dangote gwiwa kan hubbasar da yayi.

Peter Obi yace, zuba hannun jari cikin harkar mai a Najeriya ta hanyar gina matatar mai dake daya daga cikin manyan matatun mai a duniya babbar nasara ce ga al'umma da ma kasa baki daya.

Obi ya kara da cewa duk lokacin da mutum kamar Aliko Dangote zai yi kokarin kawo canji a wata harkar kasuwanci a Najeriya, dole ne ya shirya wa babban kalubale ko yanzu ko wata rana.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.