• 17 Jun, 2025

Ni Ba Mai Safarar Muggan Kwayoyi Ba Ne, Ina Da Mutunci Na—Martanin Atiku Abubakar Ga Shugaba Bola Tinubu

Ni Ba Mai Safarar Muggan Kwayoyi Ba Ne, Ina Da Mutunci Na—Martanin Atiku Abubakar Ga Shugaba Bola Tinubu

1000009885.jpg

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi wa shugaba Bola Tinubu kaca-kaca, inda ya kira Tinubu dilan kayan maye kuma maketaci.

Atiku ya furta wadannan kalaman ga shugaba Bola Tinubu ne a maida martaninsa kan cewa Atikun na hasada da mulkin Bola Tinubun.

Fadar shugaban kasar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasan Atiku ya gaza cin zabe bayan ya nemi mulkin kasar har sau shida, shiyasa ya ke hasada da shugaba Tinubu.

Atiku Abubakar wanda dan takarar shugabancin kasar ne a shekara ta 2023 karkashin jam'iyyar adawa ta PDP ya ce Najeriya ba ta taba yin Shugaban kasa da baida alkibla irin Bola Tinubu  ba.

A nata bangaren, fadar shugaban Najeriya  ta ce, rashin manufofi masu kyau da jiji da kai su ne su ka hana Atiku zama shugaban kasa.

Atiku Abubakar wanda ya maida martanin ta bakin mai magana da yawunsa Phrank Shaibu a wata takarda ya ce, babu wani abin kyashi a mulkin Bola Tinubu da baida alkibla.

Shaibu ya ce, Atiku ba dan maye ba ne kuma har abada ya fi karfin Tinubu domin Atiku na da mutunci a idanun duniya ba kamar Tinubu mai arkalla da muggan kwayoyi ba.

Atiku Abubakar ya kara da cewa Najeriya ba ta taba samun mugun shugaba irin Tinubu ba, inda ya yi alkawura da dama amma ya gaza cika guda daya.

Atiku ya ce yan kasar na cikin masifar yunwa da talauci, inda Bola Tinubu ya yi alkawari zai cire kudin shigoda abinci cikin kwanaki 150, amma yanzu haka an shafe kwanaki 120 shiru kakeji.

Atiku ya ce, babu wani alkairi da mulkin Tinubu ya kawo wa Najeriya face wahalhalu da koma bayan tattalin arziki da tsadar rayuwa da rashin tabbas cikin watanni 18 da ya hau karagar mulkin kasar.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.