
Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri ya ce, yayi mamaki kan rahoton da ke zargin sojojin Najeriya da hannu wajen satar mai a yankin Naija Delta da ke kudu maso kudancin kasar.
Gwamna Diri ya furta haka ne yayinda ya marabci rundunar hadin gwiwa ta sojan Najeriya wanda Manjo Janar Jamil Jimoh ya jagoranta a gidan gwamnatin jihar a birnin Yenagoa.
Gwamnan a jiya Litini ya bayyana bacin ransa da zargin da a ke yi wa sojojin Najeriya kan hannu dumu-dumu a cikin sace-sacen da fasa bututun mai a yankin.
Douye Diri ya ce, babu ranar da za a kawo karshen satar man matukar jami'an tsaro wadanda za su kawo karshen matsalar sunada hannu a cikin aika-aikan.
Gwamna Douye Diri ya ce, duk da haka, gwamnatin jihar Bayelsa za ta ci gaba da aiki tare da hedikwatar tsaron Najeriya don kawon karshen zagon kasar da ake yi wa albarkatun man fetur a yankin.
Mai magana da yawun gwamna Douye Diri, Mr Daniel Alabrah a cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai ya rawaito gwamna Diri na cewa, yayi farin ciki da jagorancin sojojin Najeriya ke yi kan yaki da satar man duk da zargin da ake musu.
Gwamnatin jihar ta ce tanada kwarin gwiwa cewa hadin kai tsakanin jihar Bayelsa da rundunar sojojin Najeriya zai kawo sauyi wajen rage satar mai a yankin.
Diri ya kara da cewa jihar Bayelsa na shirye don kara kaimi wajen kawo karshen sata tare da lalata kadarorin mai da makiya ke yi a jihar da ma yankin Naija Delta baki daya.
Gwamnatin jihar Bayelsan ta kara da cewa za ta dauki nauyin wayarwa mutane kai dangane da hadarin da ke tattare da satar man a yankin mai arzikin man fetur.