
Mai bawa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu
Ribadu ya ce tattalin arzikin Najeriya na bunkasa tun bayan hawan Shugaba Bola Tinubu karagar mulkin kasar.
Malam Nuhu Ribadu ya furta haka ne a wani taro na manyan jami'an hukumar kula da fasakwauri a Abuja.
Malam Ribadu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi kokarin nemo sa hannayen jari na kudi sama da Dala biliyan 30 daga kasashen ketare.
Nuhu Ribadu ya ce Najeriya ce kasa ta hudu a nahiyar Afrika ta fuskar tattalin arziki bayan kasar Egypt da Algeria, a wannan shekarar, inda hakan ya biyo bayan kokarin Shugaba Tinubu ne.
Ribado ya kara da cewa burin shugaban kasa Bola Tinubi shi ne gina tattalin arziki mai dorewa na triliyoyin Daloli nan da shekara ta 2030.
Rabadu ya ce masu sa hannayen jari da su ka ja baya na duba yiwuwar dawowa kasar domin sa ke sa hannayen jarin nasu a Najeriya.
Shugaba Tinubu a cewar Malam Nuhu Ribadu na yin hubbasa kan janyo masu sa hannayen jari daga nahiyar Asiya musamman kasar India da China domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Tinubu ya ce kasar Saudi na daga cikin.kasashen da ke da zummar sa hannun jari a Najeriya a harkar mai da iskar gas da noma da ma ababen more rayuwa.