• 18 Jun, 2025

Najeriya Na Bukatar Shugaban Kasa Na Gari A Yanzu Ko Wani Kabila Ne Shi—Cewar Obasanjo

Najeriya Na Bukatar Shugaban Kasa Na Gari A Yanzu Ko Wani Kabila Ne Shi—Cewar Obasanjo

1000004241.jpg

Wata tawagar mutum 20 ta shugabannin arewacin Najeriya karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau sun gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta.

Tawagar a jiya Talata  ta je gidan tsohon shugaban kasar ne da manufar nemo hanyoyin magance matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya da ma faɗin kasar baki daya.

Tsohon shugaban Najeriyan ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yadda rarrabuwar kai tsakanin yan kasar ya jawo komabaya.

Obasanjo ya ce duk da wadannan matsaloli da Najeriya ke fuskanta, har yanzu yana da kyakkyawan fata kasar za ta farfado wata rana idan aka daura niyya.

Obasanjo ya ce matukar za a fahimci matsalolin kasar kuma a dauki hanyar da ta dace, za a iya gyara ta.

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa, tunda kasar ta samu yancin kai ta samu shugabanni guda uku kuma tun wancan lokacin har yanzu ake tafiya cikin tsarin kasashe uku a cikin kasa guda daya, wanda hakan a cewar Obasanjo babbar barazana ce ga Najeriya.

Obasanjo ya ce duk da yana alfahari shi dan kabilar Yarbawa ne, Najeriya ba kabilanci ta ke bukata ba a yanzu, ta na bukatar shugabanci na gari ne.

Obasanjo ya ce ya zama dole kasar ta samu wanda zai iya jagorantar ta yadda yakamata ko wanene shi batare da bambamci ba, domin Najeriya ce gaba da kowa.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.