• 17 Jun, 2025

Najeriya Ka Iya Fuskantar Masifar Yunwa Idan 'Yan Kasa Ba Su Koma Ga Ubangiji Ba—Cewar Pasto Mbaka

Najeriya Ka Iya Fuskantar Masifar Yunwa Idan 'Yan Kasa Ba Su Koma Ga Ubangiji Ba—Cewar Pasto Mbaka

1000008756.jpg

Sanannen Malamin addinin Kiristan nan a Najeriya Ejike Mbaka, ya yi kira ga yan kasar da su dukufa kan addu'o'i domin samun sauki daga masifar yunwa da ke tunkarar kasar nan gaba.

Mbaka ya furta haka ne yayinda ya ke jawabi a wajen bude wani katafaren gidan mai na kamfanin Blessed Ommemma da ke garin Abakpa-Nike da ke jihar Enugu.

Mbaka ya ce, duk da cewar yan Najeriya na fama da matsalar yunwa, matsalar yunwar da ke tafe nan gaba zai yi muni fiye da wadda ake ciki yanzu.

Mbaka ya ce, akwai bukatar mahukunta su bada tasu gudumawar ta hanyar gudanarda mulki mai nagarta ba tare da almabazzaranci da dukiyar jama'a ba domin gujewa illar matsalar yunwan da ke tunkarar kasar.

Mbaka ya ce akwai bukatar 'yan Najeriya su guji ajiye kudade a bankuna duba da faduwar darajar da kudin ke yi a kowace ranar a Najeriya.

Malamin Majami'ar ya kuma ja hankalin gwamnati da ta fara duba yadda za ta rage radadin yanayin da ake ciki a kasar don kada lamarin ya ta'azzara.

Ejike Mbaka ya kara da cewa gwamnatin Najeriya na sane da yanayin da ake ciki na tsananin rayuwa a kasar kuma ta san mafita amma ta zuwa idanu ta na kallo.

Tunda gwamnatin Najeriya  ta san halin da ake ciki a cewar Mbaka amma ta gaza yin wani abu akan lamuran, mafita kadai shi ne addua daga yan kasa domin neman saukin rayuwar da yan Najeriya ke ciki.
 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.