• 17 Jun, 2025

Na Fice Daga Tafiyar Kwankwasiyya—Cewar Dan Majalisa Madaki

Na Fice Daga Tafiyar Kwankwasiyya—Cewar Dan Majalisa Madaki

1000007924.jpg

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, Ali Sani Madakin Gini ya ce ya fita daga cikin tafiyar Kwankwasiyya a cikin jam'iyyarsa ta NNPP.

Dan majalisar mai wakiltar Dala da ke cikin birnin Kano ya tabbatar da haka ne bayan wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda a ciki ya bayyana cewar ya daina tafiyar Kwamkwasiyya.

Dan majalisar tarayyar Ali Madakin Gini ya ce, tafiyar Kwankwasiyya babu wani abu face karya da yaudara.

Ali Madakin Gini ya kara da cewa ya fice daga tafiyar ce bayan ya fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya  domin ci gaban Rabiu Musa Kwankwaso kadai.

Kawo yanzu dai ba a ji wani martani daga bangaren Sanata Kwankwaso ba a kan wannan batun saga Ali Madakin Gini.

Duk da ficewar Ali Madaki daga tafiyar Kwankwasiyya, ya ce har yanzu yana nan a jam'iyyar NNPP, amma ba karkashin jagorancin Kwankwasiyya na  Rabi'u Kwankwaso ba.

Matakin na Masaki na zuwa ne kwanaki kadan bayan zaben shugabannin kananan hukumomin jihar Kano, wanda jam'iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar Ali Madakin Gini ya bawa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, shawara da ya tsaya da kafarsa ta hanyar yin jifa da tafiyar Kwankwasiyya mara yanci.

A kwanan baya ne dai wata kungiya ta bullo a fagen siyasar Kano mai taken Abba Tsaya da kafarka, wanda hakan na nufin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa.

Lamarin da ya janyo jam'iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina bisa zarginsu da alaka da kungiyar.

Ko yaya za ta kaya a wannan sabon rigimar da ta bullo kuma ta ke kokarin kassara tafiyar Kwankwasiyya? lokaci ne kadai alkalin.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.