
Rundunar hadin kai na sojin Najeriya sunyi nasarar ceto wata daga cikin 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram suka kama a watan hudun shekarar 2014.
Yarinyar da aka ceto daga hannun Boko Haram mai suna Ehi Abdul ta bayyana cewa 'yan Boko Haram sun tilasta mata auran 'yan kungiyar har guda takwas kuma a yanzu haka tanada kananan yara biyu da cikin wata uku.
Rundunar yayin aiki tukuru, sun yi nasarar ceto a kalla mutum 332 daga magarkamar kungiyar Boko Haram, inda suka mika su hannun gwamnatin jihar Borno.
Rundunar sun bayyana cewa, daga cikin mutum 332 da suka ceto, mutum 110 mata ne, mutum 222 kuma yara ne. Sojojin sunyi nasarar ceto su ne a yankin dake tsakanin Bama da Pulka kusa da dajin Sambisa a jihar Borno.
Yayin mika su ga hannun gwamnatin jihar Borno a barikin soja na Maimalari dake birnin Maiduguri, shugaban rundunar hadin kai na sojojin Manjo-Janar Waheed Shuaibu ya ce, Ehi Abdul mai shekaru 27 dake dauke da cikin wata uku na wani dan Boko Haram, sun ceto ta ne tun ranar 23 ga watan Yuni tare da yaran ta biyu.
A lokacin da take ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri, Ehi ta ce, ta yi tafiya a kafa na kwanaki da dama kafin ta riski sojojin Najeriya, inda suka dauko ta da yaran ta biyu zuwa Maiduguri.
Ehi ta kara da cewa, ba dukan su 'yanmatan chibok aka ajiye a sansani daya ba. Boko Haram sun ajiye su a gurare daban-daban.
Ehi Abdul ta ce, batasan dalilin da ya hana ragowar 'yanmatan tserewa ba, amma a fahimtar ta, wasu 'yanmatan suna son zama a dajin Sambisan tare da 'yan kungiyar ta Boko Haram, yayin da wasu kuma ba su samu damar tserewa ba.
Ta ce, batason ta yi magana akan karatun ta, amma ba ta tunani za ta sake komawa makaranta a rayuwar ta.