• 17 Jun, 2025

Mutum 5 Sun Halaka A Legas

Mutum 5 Sun Halaka A Legas

Mutum 5 Sun Halaka A Legas

2-storey-building-collapses-during-downpour-in-lagos.jpeg

Mutum 5 sun rasa rayukan su sakamakon rushewar wani gini a birnin Eko, kudu maso yammacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a yau Alhamis a rukunin gidaje dake unguwar Arowojobe, a yankin Maryland a Jihar ta Legas.

Jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Olufemi Oke-Osanyintolu ne ya bayyana hakan bayan an zakulo mamatan a baraguzan ginin da ya rushe.

Jihar Legas dai tayi kaurin suna wajen rushewar gine-gine a cikin shekarun nan, inda a baya wani bene mai hawa 21 ya rushe yayi sanadin mutuwar mutum 42.

Shugaban hukumar agajin ta jihar Legas Oke-Osanyintolu ya ce, mutane uku da suka rasu daga iftila'in ma'aikatan ginin ne.

Hukumar ta ce, an garzaya da wadanda suka samu raunuka asibitin Gbagada dake birnin Ekon domin basu magani.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.