• 18 Jun, 2025

Mutanen Maiduguri Za Su Iya Fiskantar Matsalar Abinci

Mutanen Maiduguri Za Su Iya Fiskantar Matsalar Abinci

fb-img-17260869745019181.jpg


Akwai yuwuwar mazauna birnin Maiduguri za su fiskanci barazanar karancin abinci sakamakon Ambaliyar ruwa da ta kassara birnin.

Dubannin mutane ne a Maidugurin ke fafatukar tsira da rayukan su bayan iftila'in ambaliyar da ta girgiza birnin.

Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta hadiye kayayyakin abinci kamar hatsi da kayan marmari da sauran su a kasuwannin birnin na Maiduguri.

Yayin da ambaliyar ta cinye kayayyakin abinci da ke kasuwannin, shagunan da ke sayar da sauran kayayyakin na rufe.

Hakan ya sa farashin ragowar kayayyakin abinci ya fara tashin gwauron zabi.

Matsalar ambaliyar ta shafi fannin kiwon lafiya, inda asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri ke cikin ruwa tsumbul.

Hakan ka iya kawo tabarbarewar harkar kiwon lafiya a birnin na Maiduguri da ma jihar ta Borno baki daya, inda yanzu haka an fara samun barkewar cutar Kwalara.

Ambaliyar ta tono gawawwakin mamata daga babban makabartar Maiduguri zuwa sassan birnin.

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulun tuni ya fara rabawa wasu daga cikin wadanda ke sansanin da aka samar kudade, yayin da suke jiran kayayyakin abinci.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.