
Mutane 113 sun tsallake rijiya da baya a filin tashi da saukan jiragen sama na birnin Yola a jihar Adamawa.
Kamfanin a karshe ya jinkirta tafiyar inda ya tilasta pasinjoji jiran rashin tabbas a filin jirgin na kasa-da-kasa dake birnin Yola.
Jirgin mallakar kamfanin Max Air mai dauke da pasinjoji 113 yayi yunkurin tashi daga Yola zuwa Abuja ne misalin karfe 5:15 na yammacin jiya yayin da aka fahimci tayoyin sa biyu na da matsala.
Pasinjojin sun bayyana cewa, sun gode Allah da ya kare su daga hatsarin jirgin sama.
Wani jami'in hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya FAAN, wanda ya bukaci a sakaya sunan shi ya ce, saida suka dauko tayoyin jirgi daga Abuja zuwa Yola.
Jami'in ya kara da cewa, suna duk kokarin da ya kamata don su shawo kan lamarin cikin hanzari.