
Hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa-da-kasa ta yi hasashen cewa a kalla mutane miliyan uku da digo biyu za su iya rasa matsugunan su sakamakon ambaliyar ruwan sama a wannan shekaar
Sakon hukumar wata yunkuri ne na fadakar da jama'a barazanar da ke tafe domin su shirya.
Hukumar ta ce akwai bukatar kudi dala miliyan 12.95 don samar wa masu karamin karfi sabbin matsugunni saboda kauce wa hatsarin ambaliyar a wannan shekarar.
Za'ayi amfani da kudaden ne ta hanyar tunkarar mafita daga barnar da annobar ambaliyar za ta haifar.