
Wani mummunan hatsarin mota ya hallaka mutane da dama a yankin.Agboko/Ajao da ke birnin Ibadan kudu maso yammacun Najeriya.
Shaidun gani da ido sun ce babbar motar daukan kaya ce ta kwace da hau kan kananan motoci uku.
An kai wa wadanda ke ciki motocin uku dauki inda aka yi nasarar ceto wasu daga ciki aka garzaya da su asibiti domin basu magani.
Hatsarin dai ya jawo cunkoson ababen hawa a kan titin da lamarin ya faru, amma jami'an kare hadura da yan sanda da sauran masu damara na kokarin rage cunkoson.