• 17 Jun, 2025

Mutane 228 Sun Rasa Matsugunin Su A Sakkwato

Mutane 228 Sun Rasa Matsugunin Su A Sakkwato

Mutane 228 Sun Rasa Matsugunin Su A Sakkwato

screenshot-20240722-130918-1721650673832.jpg

Akalla mutane 228 sun rasa muhallan su sakamakon ambaliyar ruwan sama a Jihar Sakkwato, arewa maso yammacin Najeriya.

Iftila'in ambaliyar ya afku ne a Karamar hukumar Gada dake jihar ta Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa jama'a sun rasa gonaki da ma dabbobin su a ambaliyar.

Dantudu da Balakozo da Gidan Tudu da Tsitse na daga cikin yankunan karamar hukumar da suka  fada cikin iftila'in.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato  NEMA ta tabbatar da faruwar lamarin a Karamar hukumar ta Gada a jihar Sakkwato.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.