• 18 Jun, 2025

Mutane 122 Sun Rasu A Sabbin Hare-Haren Boko Haram Cikin Watanni Biyu

Mutane 122 Sun Rasu A Sabbin Hare-Haren Boko Haram Cikin Watanni Biyu

2024-09-03t193732z-1920385960-rc2zs9aamibb-rtrmadp-3-nigeria-security-1725418732.webp

A wani abu mai kama da sabon hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, a kalla 'yan kungiyar sun hallaka mutum 122 cikin watanni biyu da 'yan kai.

Bangaren ISWAP na kungiyar sun kai hare-haren ne a jihohin Yobe da Borno cikin kauyukan da suka shafe shekaru da dama suna zaman lafiya.

Duk da cewa rundunar sojan Najeriya da ma sauran cibiyoyin tsaro sunyi kokari wajen kassara ta'addancin 'yan kungiyar, an jefa mutane a cikin rudani game da sabbin hare-haren ta'addancin 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Yan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare da dama cikin wadannan watannin biyu, inda suka hada da harin garin Mafa da Geidam a jihar Yobe a watan da ya gabata na Agusta da wannan wata na Satumba.

Tambayar ita ce, ko rundunar tsaro ta kasa ta shirya sabon dabarun tunkarar sabbin hare-haren kungiyar ta Boko Haram ko kuwa?

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.