
Dan'uwan tshohon hafsan sojan Najeriya Pa Tajudeen Lagbaja ya ce, ya yi da-na-sani da ya kyale marigayi Taoreed Lagbaja ya shiga aikin soja.
Pa Tajudeen Lagbaja ya ce, shigan dan'uwansa aikin soja ne ya yi sanadin mutuwarsa.
Tajudeen ya ce, maimakon haka, da shi ne ya shiga aikin sojan ba dan'uwansa Taoreed ba.
A daya bangaren, wasu daga cikin 'yan'uwan Taoreed Lagbaja sun yi zargin an kashe Taoreed Lagbaja ne sakamakon rikicin fili da ya yi da wasu a kauyensu.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon hafsan sojan Taoreed Lagbaja ya yi wata rigima a shekarar da ta gabata ta 2023 kan fili a garin Ilobu, hedikwatar karamar hukumar Irepodun da ke jihar Osun.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu wakilan rundunar sojan Najeriya ne suka bukaci gina asibiti a filin, wanda hakan ya shafi Taoreed Lagbaja a matsayinsa na shugaba.
Pa Tajudeen ya ce, duk da cewa mutuwa ta zama dole kuma sun mika kaddararsu ga ubangiji, amma mutuwar dan'uwan nasu ya musu zafi matukar.
Tajudeen ya kara da cewa Taoreed Lagbaja mutumin kirki ne, domin yayi ayyukan alheri da dama, wanda suka hada da gina rijiyar burtsatsi a cikin gidan mahaifinsa da gurare da dama.