
Kamfanin sadarwar wayar tafi-da-gidan ka na MTN ya samu cikas daga wayoyin layukan sadarwa da ke karkashin kasa a Najeriya.
Kamfanin ya ce sama da wayoyinsa dubu sittin su yanke tsakanin shekarar 2022 da 2023, inda kamfanin ya yi asarar kadara da ya kai na zunzurutun kudi Naira biliyan 11.
Kamfanin ya ce ya kaurar da wayoyin sadarwar da suke da nisar kilomita 2,500, inda suka kashe kudi sama da Naira biliyan 11.
MTN sun bayyana cewa aikin ya lashe musu makudan kudi da za ta iya gina sabon layin sadarwa na tsawon kilomita 870 inda babu sadarwa a Najeriya.
Masu masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa a Najeriya sun nemi gwamnatin tarayya ta yi wani abu domin ceto kayayyakin sadarwar.
Masanan sun kuma ja hankalin gwamnatin Najeriya ta duba matsalar sace-sacen kayayyakin da ma lalata su da bata gari kebyi a kasar domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Masu ruwa da tsakin sun kara da cewa, akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta karbi harkar tsaron kadarorin sadarwar wayar salula a kasar duba da muhimmanci sa.