• 17 Jun, 2025

Muna Bukatar Karin Jarin Kudi Dalar Amurka Miliyan 500—Cewar Kamfanin Lantarki Disco

Muna Bukatar Karin Jarin Kudi Dalar Amurka Miliyan 500—Cewar Kamfanin Lantarki Disco

1000010702.jpg

Gamayyar kamfanonin samarda lantarki a Najeriya DisCos sun bayyana cewa suna bukatar karin jarin zunzurutun kudi har Dalar Amurka miliyan 500 domin inganta hasken wutar lantarki a fadin kasar.

Manajan tashar wutar lantarki na Azura a nahiyar Afrika ta yamma Edu Okeke ne ya furta bukatar ta su, inda ya ce kamfanin wutar na DisCos na da rauni sosai wajen gudanar da ayyukansa.

Yayinda ya ke jawabi a wajen taron karawa juna sani na kamfanonin samarda lantarki karo na hudu a Abuja jiya Alhamis, Okeke ya ce, duk da karin kudin lantarki da su ka yi, har yanzu kamfanonin lantarkin na fama da matsalolin kudade.

Okeke ya ce, ya zama wajibi hukumar wutar lantarki ta kasa NERC ta duba yiwuwar bawa kamfanonin lantarkin tallafin kudaden kamar yadda babbar bankin kasa ke tallafawa bankunan 'yan kasuwa domin kawo canji a harkar samarda lantarki a Najeriya.

Okeke ya kara da cewa babu wani kamfanin lantarki da zai tsaya da kafarsa ba tare da tallafin gwamnati ba.

Okeke ya ce duk da cewar sun yi karin kudaden shan wutar lantarkin a Najeriya, bukata ba ta biya ba, domin suna son kiarin kudi kuma, inda Okeke ya ce wajibi ne gwamnati ta shiga lamarin.

Manajan ya ce, a takaice ya kamata kamfanin lantarki ya mallaki jarin kudi da ya kai Dalar Amurka miliyan 250 domin ayyukan samarda lantarki, amma hakkan bai yiwu ba.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.