
Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya ce, daga watan Janairu na shekarar 2025, gwamnatin jihar za ta fara daukar nauyin jinyar masu fama da cutukan suga da hawan jini da sikila a fadin jihar.
Namadi ya ce, gwamnatin sa za ta yi amfani da asibitocin gwamnatin jihar ta Jigawa domin kulawa da masu dauke da cutukan.
Umar Namadi ya nuna damuwarsa kan yadda cutukan ke karuwa cikin al-umma musamman marasa galihu a jihar.
Gwamna Namadi ya furta haka ne a ranar Alhamis yayinda ya ke jawabi a wani taron shekara-shekara da kungiyar likitocin Najeriya ta NMA ta shirya a garin Hadeja da ke jihar, domin fadakarwa kan illar cutar koda.
Gwamnan wanda kwamishinan lafiya na jihar Abdullahi Kainuwa ya wakilta ya ce Gwamnatinsa ta kammala dukkan shirye-shirye domin bude cibiyoyin wanke koda a birnin Dutse da Hadeja da Kazaure da Ringim da Gumel a watan Maris na shekarar 2025.
Kwamishinan lafiyan jihar ta Jigawa Abdullahi Kainuwa ya ce, a matsayin shi na likita, ya san illolin da cutar suga da hawan jini ke haifarwa, domin suna haddasa cutar koda mai tsanani.
Kwamishinan ya ce, dalilin da ya sa kenan gwamnatin jihar Jigawa ta ga akwai bukatar ta shiga lamarin domin tallafawa masu tattare da cutukan.