• 18 Jun, 2025

Mun Shirya Domin Fara Sayar Da Tataccen Man Petur—Cewar Aliko Dangote

Mun Shirya Domin Fara Sayar Da Tataccen Man Petur—Cewar Aliko Dangote

al-shabani-at-the-acquisition-of-dangote-cement-by-icd-in-2014-cropped-1.jpg


Aliko Dangote ya bayyana cewa matatarsa da ke birnin Lagos ta shirya   fara sayar da tataccen man fetur da disel wa gidajen mai a Najeriya.

Shugaban ya ce masu harkan jigilar man petur za su iya samun man daga matatarsa da ke birnin Eko sakamakon aiki tukuru da ya yi wajen ganin matatar ta kammala.

Dangote ya ce, a yanzu 'yan kasar baki daya za su fara samun tataccen man petur daga danyen man da ake hakowa a kasar.

Matatar man na Dangote ta fara tace man ta cikin makon da ya gabata domin kawo karshen matsalar fidda danyen mai kasashen ketare da sunan tace wa.

Yanzu haka dai 'yan Najeriya na ta korafi sakamakon karin farashin man petur da kamfanin mai na kasa NNPC ta yi a wannan makon inda kudin litar mai guda ta kai har Naira 800 a kasar da Allah ya azurta ta da albarkatun mai a nahiyar Afrika.

Abin jira a gani dai shi ne ko matatar man Aliko Dangote za ta kawo canji ta fiskar wahalar samun man da ma tsadar sa ko akasin haka.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.