
Jagoran kungiyar kare hakkin matasa ta kasa Micheal Lenin ya bayyana yadda jami'an 'yansanda su ka azabtar da shi da sauran wadanda aka kama a cikin magarkama.
Lenin ya ce mutane da dama na fuskantar hukuba a hannun 'yansandan Najeriya wanda hakan babbar kalubale ce ga 'yancin dan'Adam a kasar.
Micheal Lenin na daya daga cikin wadanda aka kama aka tsare sakamakon zanga-zangar rashin gwamnati mai nagarta da aka gudanar a watan Agustan wannan shekara.
An saki Lenin bayan ya shafe watanni a magarkamar 'yansandan Najeriya, inda ya bayyana abubuwan firgitarwa a ranar farko da ya shiga hannun 'yansanda, duk da cewa a sabon magarkama aka ajiye su.
A lokacinda aka kaishi wani waje a cikin magarkamar, ma'aikatan sun yi korafi kan lalacewar lamura a kasar, inda su ka bayyana cewa abubuwan da ya ke yi abu mai kyau ne.
Micheal Lenin ya ce su 30 aka tsare a magarkamar, inda mutane su ka koka yanayin magarkamar da babu kulawa sa'annan babu abinci.
Micheal ya ce wasu sun samu raunuka sakamakon azabtarwa a hannun jami'an tsaro. Ya ce, wasu raunukan na wari ba tare da an yi musu jinya ba.
Lenin ya kara da cewa yayi kwana uku ba tare da an bashi abinci ba, yayinda jami'an tsaron ke karbe kudaden da aka ba su. Micheal ya ce, babu abinci kuma babu kudaden su.