• 18 Jun, 2025

Mulkin Najeriya Na Da Sarkakiya Amma Ba Wahala—Cewar Obasanjo

Mulkin Najeriya Na Da Sarkakiya Amma Ba Wahala—Cewar Obasanjo

obasanjo-pose-696x607-1-2.webp

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya kasa ce mai sarkakiya wajen mulki a nahiyar Afrika.

Obasanjob ya ce duk da haka kasar na da saukin gudanar wa idan shugaba na da kwarewa da kyakkyawar niyya.

Obasanjo ya furta haka ne a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da marigayi Akintola Williams a birnin Legas kudu maso yammacin Najeriya.

Obasanjo ya kara da cewa adalcin shugaban kasa ga 'yan kasa tare da tsoron Allah ne kadai shugabanni suka rasa shiyasa mulkin kasar ke basu wahala.

Ya bayyana cewa ya zama shugaban kasa a shekarar 1999 inda ya shafe shekaru 8 amma yayi iya kokarinsa wajen daidaita basukan da kasar ke karba daga ketare da abinda kasa ke samu a matsayin kudin shiga.

Obasanjo ya ce babu wata tazara sosai tsakanin kudin da ke asusun ajiya na kasa da kudin da ake biyan basukan da aka ciwo, amma duk da haka yayi kokari batare da ya jefa kasar cikin masifar da ta ke ciki a yau ba.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.