• 17 Jun, 2025

Mulkin Bola Tinubu Ne Mafi Lalacewa A Tarihin Najeriya—Cewar Obasanjo

Mulkin Bola Tinubu Ne Mafi Lalacewa A Tarihin Najeriya—Cewar Obasanjo

1000011147.jpg

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya soki salon mulkin shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya ce kasar ta sukurkuce karkashin Tinubu.

Obasanjo ya bayyana cewa babu wani abu a mulkin Tinubu face rashawa da gazawa da rashin tabbas na gobe da jibi.

Obasanjo ya furta haka ne yayinda ya ke jawabi a wajen wani taro a jami'ar Yale da ke Haven a Connecticut a kasar Amurka.

A wata takarda da mai magana da yawun sa Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya kira Shugaba Bola Tinubu da mai tafiyar hawainiya wajen yin abubuwan kawo canji a fannin tattalin arzikin kasa.

Yayinda ya ke jawabi akan maudu'i mai taken "lalacewar Najeriya," Obasanjo ya yi gargadin cewa Najeriya na nitsewa  cikin mummunar rashin tsaro, rarrabuwar kai tsakanin 'yan kasar da  cin hanci da rashawa a gwamnatin Bola Tinubu.

Obasanjo ya ce duk lokacin da rashawa da tsaro da rikice-rikice su ka yi yawa a kasa, tabbas kasar za ta ruguje, kamar halin da Najeriya ke ciki a yanzu.

Rashin shugabanci na gari ne ya haddasa dukkan matsalolin Najeriya, musamman salon mulkin shugaba Tinubu, a cewar Obasanjo.

Obasanjo ya zargi manyan 'yan siyasar kasar da hannu cikin lalacewar Najeriya, inda ya ce, da hadin bakinsu ake ruguza kasar ta hanyar karya dokokin kasa da bijiro da tsare-tsare marasa amfani.

Tsohon shugaban ya zargi manyan 'yan siyasar da sauran masu fada aji da hannu dumu-dumu a magudin zabe da sayan kuri'u da maida kasar mallakinsu ba tare da duba dubun jama'ar kasar da ke cikin wahalhalu ba.

Obasanjo ya ce, duk da haka, za a iya warware matsalolin Najeriya idan aka samu shugabancin mai nagarta da adalci da gyare- gyaren da su ka wajaba.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.