
Shugaban Kungiyar Kwadagon Najeriya ya ce, su ne suka ki amincewa da mafi kankanci sabon albashi ma'aikata na Naira dubu 250 ba gwamntin tarayya ba.
Shugaban Joe Ajaero ya ce, gwamnatin Bola Tinubu ta amince da butar su na mafi kankancin abashin na Naira 250,000 amma kungiyar ta ki amincewa da garabasar.
Joe Ajaero ya ce, sun dauki matakin ne saboda gwamnatin ta bada sharadin cewa dole za ta sake kara kudin mai a kasar idan har za ta biya mafi kankanci albashin Naira 250,000.
Shugaban kungiyar kwadagon ya ce, duba da hakan ne suka zabi Naira 70,000 maimakon karin kudin mai bayan biyan albashi 250,000.
Ya ce, ya na da yakinin ma'aikatan Najeriya za su so 70,000 mai albarka maimakon 250,000 da karin kudin mai zai biyo baya.