• 18 Jun, 2025

MTN Sun Fara Bude Wasu Layukan Jama'a Da Suka Toshe

MTN Sun Fara Bude Wasu Layukan Jama'a Da Suka Toshe

MTN Sun Fara Bude Wasu Layukan Jama'a Da Suka Toshe

mtn-logo-2002-768x432.png

Kamfanin sadarwa na wayar tafi-da-gidan ka MTN a Najeriya ya fara budewa mutane layukan wayoyin salular su a kasar.

Idan ba'a manta ba kamfanin ya toshe wa dubannin daruruwan jama'a layukan su a karshen makon da ya gabata.

Kamfanin ya dauki matakin ne a cewar sa sakamakon yin biris da yan Najeriya suka yi kan bukatar kowa ya hada layukan sa da lambar katin shaidan dan kasar sa NIN.

Daga bisani dai kamfanin MTN yayi amai ya lashe, inda ya fara budewa mutane layukan su da ya riga ya toshe a karshen makon.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta ma'aikatar sadarwa ce ta bawa Kamfanin  MTN umarnin bude layukan wayoyin yan kasar na tafi-da-gidan kan.

A karshe dai wasu daga cikin dunbun yan Najeriya da aka toshe layukan su yanzu haka sun fara amfani da layukan kamar yadda suka saba bayan sun shiga mummunan hali sakamakon toshe layukan.

Yan kasar da dama sun shiga damuwa bayan Kamfanin MTN sun toshe layukan nasu. Mutane da dama sunyi asara, inda aka hana su damar gudanar da harkokin cinikayya da kira da tura sakonni da ma shiga yanar gizo.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.