• 18 Jun, 2025

Ministan Tinubu Ya Roki Yan Jihar Sa Su Ajiye Zanga-Zanga

Ministan Tinubu Ya Roki Yan Jihar Sa Su Ajiye Zanga-Zanga

Ministan Tinubu Ya Roki Yan Jihar Sa Su Ajiye Zanga-Zanga

screenshot-20240731-081203-1722418975776-1722418993529.jpg

Ministan albarkatun ruwa da tsafta Farfesa Joseph Utsev ya roki yan jihar Benue su hakura da shiga zanga-zangar da za'a fara gobe Alhamis a fadin Najeriya.

Farfesa Joseph Utsev ya mika rokon nasa ne a birnin Makurdi yayin da yakai ziyarar raba takin zamani da na'urorin bawa gonaki ruwa da sauran kayayyakin noma a jihar.

Ministan yace shugaban Kasa Bola Tinubu na da masaniyar halin da yan kasa ke ciki na matsin tattalin arzikin amma jama'a su kara hakuri.

Farfesa Utsev yace gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta tanadi matakai da dama wadanda za su kawo karshen wahalhalun da talaka ke ciki idan jama'a suka kara hakuri kuma suka bawa shugaban kasar karin lokaci.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin Bola Tinubu na da zummar kawo gagarumin sauyi a Najeriya idan ta samu lokaci yadda ya kamata.

Utsev yace, gwamnatin shugaba Tinubu ta bude shirin bunkasa noma ta hanyar tallafawa manoma da kayayyakin noma kyauta a jihohin kasar 36 kamar yadda ya je jihar sa ta Benue yake raba kayayyakin bunkasa noman.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.