
Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya zargi wani dan majalisar dattawa da hannu wajen ruruta zanga-zanga a kasar da aka fara jiya Alhamis.
Nyesom Wike yace dan majalisar dattawan ya tanadar wa masu zanga-zangar abinci da abin sha a Abuja domin karya doka da oda da gwamnatin birnin tarayyar ta bada.
Ministan ya furta haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaru jim kadan bayan wata ganawa kan harkar tsaro da ya yi da shugabannin jami'an tsaro a Abuja.
Duk da cewa ministan bai ambaci sunan kowa ba, yace sunada bayanan sirri kan zagon kasar da sanatan ke yi wa kokarin su na dakile zanga-zanga a kasar.
Wike yace, dan majalisar tarayyar ya ware kudade da dama don tanadar wa masu zanga-zangar abinci yayin gudanar da boren.