
Matan tsohon shugaban Najeriya Patience Jonathan ta ce mijin ta Goodluck Ebele Jonathan ba zai tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2027.
Patience ta bayyana cewa mijin ta zai bawa shugaban kasa Bola Tinubu goyon baya yadda ya kamata maimakon neman sake hawa karagar mulkin kasar.
Patience Jonathan ta furta haka ne a wajen wani taron 'yan kabilar Igbo a birnin tarayya Abuja, inda ta ce mijin na ta baya sha'awar komawa kujerar mulkin Najeriya.
Patience Jonathan ta yi kira ga 'yan kabilar Igbo su ajiye duk wani irin banbanci domin gina kasar saboda goben 'ya'ya da jikoki masu tasowa.