• 17 Jun, 2025

Mazauna Birnin Kano Sun Rungumi Kekunan Hawa Sakamakon Tsadar Man Fetur

Mazauna Birnin Kano Sun Rungumi Kekunan Hawa Sakamakon Tsadar Man Fetur

1000009654.jpg


Wasu mazauna birnin Kano arewa maso yammacin Najeriya sun ajiye motocinsu sun koma hawan kekuna da babura masu aiki da lantarki.

Hakan ya biyo bayan tsadar man fetur a kasar, inda litar man ya kai har Naira 1,150 a jihar ta Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa babu motoci a kan titunan birnin kamar yadda aka saba gani a lokutan baya.

Wani mai tafiya a kasa mai suna Sani Isa ya ce, ba kowa ba ne zai iya sayan man fetur domin sa wa a mota saboda abin ya yi tsanani.

Isa ya ce, yayinda man fetur ya yi tsada, farashin kudin hawan babur ma ya haura fiye da yadda talaka zai iya biya.

Sani Isa ya kara da cewa, lamarin babu dadi, domin ya na kashe Naira 1,200 kowace rana a sufuri kadai.

Isa ya ce, dalilin da ya sa kenan ya nemi keke domin samun saukin sufurin, duba da tsadar man ta ko ina.

Wani dalibin Kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Kano, Aminu Ishaq wanda shi ma ya rungumi keke ya ce, hakan ya fi mishi sauki saboda yanada bukatu da dama kuma yanada iyaye da ya ke kulawa da su.

Muhammad Sadiq wani ma'aikacin gwamnati ne wanda ya ce shi kam ya raba sufurinsa kashi biyu, inda rabin tafiyar a kasa ya ke yi, yayinda ya ke biyan kudin babur ya karasa ofis.

Muhammad ya ce, mutane da dama sun ajiye motoci da sauran ababen hawa masu amfani da man fetur sun rungumi keke saboda tsadar mai da 'yan kasa ke fama da ita.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.