• 17 Jun, 2025

Mayakan Hezbollah Sun Jafa Makamai Masu Linzami A Kudancin Kasar Israela

Mayakan Hezbollah Sun Jafa Makamai Masu Linzami A Kudancin Kasar Israela

1000013010-2.jpg

Mayakan Hezbollah na kasar Palestine sun jefa makamai masu linzami a sansanin sojan ruwa da ke birnin Tel Aviv a kudancin kasar Israela.

Mayakan na Hezbollah sun ce sun kai harin ne a jiya Lahadi gabanin kokarin kai hari ta sama da Israelan ta shirya yi a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Hezbollah ta ce, wannan ne karon farko da ta kai hari a kudancin Israela, inda ta ce, ta yi amfani da makaman linzami masu hadari da jiragen marasa matuka.

Sojan Israelan dai sun ce, sun yi nasarar kakkabo kayan yakin na Hezbollah guda 55 daga cikin 160 da mayakan Hezbollah suka harba musu.

A kalla mutum 11 sun samu raunuka sakamakon harin na Hezbollah akan Yahudawan kamar yadda tashar talabijin na Al-Jazeera ta ruwaito.

Harin na Hezbollah na zuwa ne kwana daya bayan kasar Israela ta kai hari Kasar Lebanon inda ta hallaka mutane 29 a birnin Beirut, yayinda mutum 66 suka samu raunuka, kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bayyana.

Mayakan na Hezbollah sun bayyana cewa, sun kai harin kasar Israela ne a matsayin maida martanin harin da kasar ta kai wa kasar Lebanon.

Hezbollah ta kara da cewa ta yi nasarar kai hari kan wani sabon dakin makamai na rundunar sojan Israelan a garuruwan Metula da Hatzor Haglilit da Ma'alot da ma Kfar Blum duka a arewacin kasar Israela.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.