
Wani matukin jirgin sama mallakar kasar Turkiya ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tukin jirgi a sararin samaniya.
Jirgin ya yi saukar gaggawa a filin tashi da saukar jiragen saman birnin New York da ke kasar Amurka bayan lamarin ya faru.
Jirgin samfurin Airbus 350 na kan hanyar sa ne na zuwa bitnin Istambul na kasar ta Turkiya ranar Talata.
Mai magana da yawun kamfanin jirgin saman Yahaya Ustun ne ya bayyana haka inda ya ce matukin jirgin mai suna Ilcehin Pehlivan ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tukin jirgin.
Abokin tukin jirgin ne ya karkata akalar jirgin tare da yin saukar gaggawa a birnin New York bayan ma'aikatan jirgin sunyi kokarin ceto rayuwar Pehlivan ta hanyar bashi agajin farko amma hakan ya ci tura.
Matukin jirgin mai shekaru 59 dai ya rasu bayan ya shafe shekaru 17 yana tukin jirgin kasar ta Turkiya.